Najeriya: An kashe mutane 645 cikin watanni shida a Kaduna
Gwamnatin jihar Kaduna dake Najeriya tace, hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai sun kashe mutane 645 a jihar cikin watanni shida, wato daga watan Janairu zuwa Yuni wannan shekara ta 2022.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoton tsaro kan tashe tashen hankula a jihar da ta fitar ranar Juma’a.
Rahoton ya bayyana cewa an kashe adadin wadan nan mutane ne a hare-haren ta'addanci da fadan kabilanci da kuma na ‘yan fashin daji.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ya ce kusan kashi daya bisa uku na wadanda aka kashe (234) an kashe su ne a Kudancin Kaduna.
“A cikin watanni shida na farkon shekarar 2022, mutane 645 ne suka rasa rayukansu a irin wannan yanayi a fadin jihar; 234 daga cikin wadannan sun faru ne a yankin Kudancin Kaduna,” in ji Mista Aruwan a wani taron gabatar da rahotannin zaman lafiya a tsakanin addinai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu