Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 10 a jihar Kaduna

Ma’aikatar tsaron cikin gida a jihar Kaduna ta Najeriya ta tabbatar da samun rahoton yadda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu daliban sakandire 10 a karamar hukumar Kachia.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan  jihar Kaduna Samuel Aruwan yayin gabatar da rahoton tsaro karo na biyu da na uku na shekarar 2022. 04/11/222
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gidan jihar Kaduna Samuel Aruwan yayin gabatar da rahoton tsaro karo na biyu da na uku na shekarar 2022. 04/11/222 © kaduna state
Talla

Majiyoyin labarai a jihar ta Kaduna sun bayyana cewa a jiya litinin ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da daliban 10 na makarantar Sakandiren gwamnati ta Awon da ke yankin karamar hukumar Kachia na jihar.

Sanarwar da ma’aikatar tsaron cikin gida a Kaduna ta fitar dauke da sa hannun kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan a yau talata ta tabbatar da garkuwa da daliban 10, sai dai ta ce har zuwa yanzu ba a kai ga gano a dai dai wajen da ‘yan bindigar suka sace daliban ba.

A cewar sanarwar jami’an tsaro na ci gaba da bincike a kokarin kubutar da yaran 10 sai dai babu tabbacin ko cikin harabar makarantar ‘yan bindigar suka shiga suka yi garkuwa da su ko kuma a wani waje daban ne da daliban suka je.

Sace daliban dai na zuwa ne kwanaki 2 bayan wasu ‘yan bindigar na daban sun sace daliban jami’a mata 2 a jihar Zamfara lamarin da ya sanya girke jami’an tsaro a kofar shiga jami’ar yau talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.