Isa ga babban shafi
Brazil

Kasashen BRICS na gudanar da taro a kasar Brazil

Yau talata kungiyar BRICS, wadda ta kunshi kasashe 5 masu samun habakar tattalin arziki a duniya, wato Brazil, China, India, Rasha da kuma Afirka ta Kudu, na gudanar da taronta na shekara shekara, domin tattaunawa batutuwa musamman ma na tattalin arziki a tsakaninsu.

Tambarin kungiyar BRICS
Tambarin kungiyar BRICS REUTERS
Talla

Taron wanda ke gudana a birnin Fortaleza na arewa maso gabashin kasar Brazil, zai kasance wata dama ga shugabannin wadannan kasashe domin ci gaba da tattaunawa dangane da kafa wani sabon banki da zai taka rawa irin wadda bankin duniya da asusun bayar da lamuni na duniya ke takawa wajen bayar da rance ga kasashe mabukata.

Sanarwar da gwamnatin kasar Brazil ta bayar, na cewa sabon bankin zai mallakin jarin da ya kai akalla dala milyan dubu 50 a cikin shekarunsa 7 na farko, yayin da bankin zai mallaki wasu kudade akalla dalla milyan dubu dari daya a matsayin asusun ajiya.

Majiyoyi dai sun bayyana cewa babbar cibiyar bankin za ta kasance ne a birnin Shangai na kasar China, yayin da Afirka ta kudu ke fatar girka cibiyar a birnin Johannesburg.

Kasashen mambobi a kungiyar ta BRICS, na da kimanin kashi 40 cikin dari na al’ummar duniya, wata alama da ke kara yin nuni da tasirin wadannan kasashe a fagage da dama cikinsu kuwa har da na siyasa da kuma na tattalin arziki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.