Isa ga babban shafi
Najeriya

An kashe ‘Yan kasar India biyu a Najeriya.

Wasu ‘Yan kasar India su biyu sun rasa rayukansu bayan wasu yan bindiga sun kai hari wata ma’aikata a garin Maiduguri da ke Arewacin Najeriya.Kamfanin Dillancin labaran Faransa ya rawaito cewa ‘yan bindigan sun kuma kwashe kudi mai yawan Dalar Amurka 600, kwatankwacin kudi Naira 99,000 a yayin da su ka kai harin. 

Wani hari da aka kai garin Damaturu a Arewacin Najeriya
Wani hari da aka kai garin Damaturu a Arewacin Najeriya Reuters/Olatunji Omirin
Talla

Babu dai cikakken bayani akan wanna hari sai dai wata sanarwa da rundunar sojin da ke samar da zaman lafiya a yankin ta ce an kuma raunata mutum daya ana kuma kula da shi asibiti.

Rundunar sojin ta kara da cewa an kewaye inda abin ya faru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.