Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka za ta shigar da makamai a Iraqi

A daidai lokacin da ya ke ci gaba da shan suka a ciki da waje sakamakon gazan kawo karshen yadda mayaka masu ikirarin jihadi ke ci gaba da kwace muhimman yankunan kasar Iraki daga hannun dakarunn gwamnati, shugaba Barack Obama ya ce Amurka za ta gaggauta bayar da horo da kuma manyan makamai ga wasu kabilun Iraqi domin kare kansu daga ‘yan bindiga.

Dakarun Iraqi da ke fada da Mayakan IS masu da'awar Jihadi
Dakarun Iraqi da ke fada da Mayakan IS masu da'awar Jihadi REUTERS/Stringer
Talla

A wata ganawa da ya yi da manyan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a fadarsa da ke birnin Washington a jiya Talata, Obama ya amince da gaggauta bayar da makamai ga mayaka ‘yan sunni domin kare sauran yankuna da ke zagaye da Bagadaza bayan fadawar birnin Ramadi a hannun mayakan IS.

Yanzu haka Iraqi tana neman mayakan sa-kai da za su bayar da gudunmuwa domin kwato birnin Ramadi daga hannun Mayakan IS.

Daruruwan mutane ne suka fice Ramadi bayan Mayakan IS sun kwace ikon garin a karshen makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.