Isa ga babban shafi
UNICEF

Yara Miliyan 14 na rayuwar kunci a Syria

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce yara miliyan goma sha hudu ke cikin rayuwar kunci sakamakon rikici kasashen Syria da Iraqi.

'Yan gudun hijirar Syria a kasar Lebanon
'Yan gudun hijirar Syria a kasar Lebanon REUTERS/Hassan Abdallah
Talla

A wani rahoton da UNICEF ta fitar, ta ce yara ‘yan kasar Syria sama da miliyan biyar da dari shida ne ke rayuwa cikin kunci, inda suke fuskantar rashin abinci da sauran kayan more rayuwa.

Hukumar ta ce akwai wasu yara sama da miliyan biyu da ke kara-zube, wadanda samun kayan agaji abu ne mai wuya a gare su balle batun samun ilimi.

Hukumar ta kara da cewa a yanzu haka akwai yara kusan miliyan biyu da ke rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira a cikin kasashen Lebanon da Turkiya da Jordan da wasu kasashen da ke makwabtaka da Syria.

Shugaban hukumar UNICEF Anthony Lake ya ce rikicin ya kasance abin da zai zauna a zukatan yaran a tsawon rayuwarsu.

Shugaban ya ce Yara miliyan biyu da dari takwas ne yanzu haka rikicin kasar Iraki ya tilastawa tserewa daga gidajensu

Wannan na zuwa ne a daidai wani lokaci da manyan kungiyoyin bayar da agaji a kasar Syria ke zargin manyan kasashen duniya da cin amanar nauyin da ya rataya a wuyansu, na rashin yin la’akari da azabar da miliyoyin fararen hular kasar Syria ke ciki tun bayan barkewar yakin basasa tsawon shekaru 4 da ya daidaita kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.