Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen Duniya sun ci amanar fararen Hula a Siriya

Manyan kungiyoyin bayar da agaji a kasar Siriya sun zargi manyan kasashen duniya da cin amanar nauyin da ya rataya a wuyansu, ta rashin yin la’akari da azabar da miliyoyin fararen hular kasar ke ciki, wadanda suka kidime sakamakon yakin basasar tsawon shekaru 4 da ya daidaitar da kasar

Talla

A cikin wani rahoto da kungiyoyin kare hakkin dan adam din 21 suka fitar a yau, sun soki kasashen duniya da kasa aiki da jerin yarjeniyoyin da komitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya cimma, na kare rayukan fararen hular, ta hanyar kin bada kayan agaji ga mutanen da ke cikin matukar bukata.

Yanzu haka dai Dakarun gwamnatin kasra Siriya na fafatawa da ‘yan tawayen kasar masu kokarin kifar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad a karkashin jagorancin kassahen Turai kamar Amurka da Burtaniya da Faransa da dai sauransu.

Kasar ta Siriya haka ma na fama da matsalar ‘yan tawayen IS da ke ci gaba da kai hare-hare da fararen Hula da basu ji ba basu gani ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.