Isa ga babban shafi
Iraqi

Mayakan IS sun kafa Tuta a Ramadi

Mayakan IS da ke da’awar Jihadi sun kafa tutoci a gine ginen gwamnati a birnin Ramadi a yau Juma’a, kuma rahotanni sun ce mayakan na dab da kwace babban birnin na lardin Anbar baki daya.

Mayakan IS da ke da'awar Jihadi a Iraqi
Mayakan IS da ke da'awar Jihadi a Iraqi Syrian Observatory for Human Rights
Talla

Mayakan IS sun dade suna barazanar karbe Ramadi, bayan sun ta kai farmaki a yankin.

Rahotanni sun ce mayakan sun karbe babbar hedikwatar gwamnati da misalin karfe 2 na rana tare da kafa tutarsu.

Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ruwaito cewa mutanen yankin na ficewa garin da kafa ba tare da dukiyoyinsu ba.

Majiyoyin tsaro sun ce Mayakan sun karbe ikon garuruwa da suka kewaye Ramadi a lardin Anbar tare da sadaukar da nasarar da suka samu ga Abu Muhannad al-Swaidawi babban kwamandan kungiyar da ke kula da lardin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.