Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Fadawar Ramadi a hannu IS hatsari ne

Amurka ta ce fadawar birnin Ramadi a hannu ‘yan tawayen IS babba hatsari ne a gabas ta tsakiya, sai dai ta ce zata marawa Gwamnatin Iraki baya domin kwato birnin a cikin gaggawa.Wannan dai na zuwa ne bayan gwamnatin iraki ta tura, Jerin motocin mayakan sojin sa kai na 'Yan Shi'a dubu 3, domin kwato birnin na Ramadi.

Mutane da ke kokarin tserewa a Ramadi
Mutane da ke kokarin tserewa a Ramadi Reuters
Talla

Tuni dai mayakan na shi’a suka isa wani sansanin a kusa da birnin Ramadi, inda suka shirya tsaf domin fatattakar ‘yan tawayen ISIL daga yankin.

Gwamnati iraki dai na fatan rundunar sojin sa kai dubu uku da ta aike za ta taimaka ta kwato birnin na ramadi da kuma dakile abin da ta bayyana a matsayin nasara mafi muhimmanci da kungiyar IS ta samu a wannan lokacin.

karbe iko Ramadi ya zama babba koma baya ga dakarun kasar Iraki al’amarin da friya minista kasar Haidara al-Abadi ya nuna nadamarsa da yin sake, na kin tura mayakan shi ‘a kewaye Ramadi a lardin Anbar tun a baya.

Mayakan 'yan Shi'a wadanda ke da alaka da Iran a kwanan nan sun taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa dakarun Iraki sake kwato yankuna da dama. Kuma ko a yanzu ma sun lashi takobin fatattakar kungiyar ta IS daga Ramadi.

A dai ranar juma’a data gabata ne Mayakan IS da ke da’awar Jihadi suka kafa tutoci a gine-ginen gwamnati a birnin Ramadi, kuma rahotanni sun ce mayakan na dab da kwace babban birnin na lardin Anbar baki daya. Tare da sadaukar da nasarar da suka samu ga Abu Muhannad al-Swaidawi babban kwamandan kungiyar da ke kula da lardin.
Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ruwaito cewa mutanen yankin sun ta ficewa daga garin da kafa ba tare da dukiyoyinsu ba.

Dakarun Sojin kasar Amurka da ke kai hare-hare akan 'yan tawayen IS a gabas ta tsakiya, sun dau alwashin bada gagarumin taimako wajen fatataka IS daga Ramadi kamar yadda mai magana a madadin Pentagon kanal Steven Warren ya sanarwa manema labarai
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.