Isa ga babban shafi
Macedonia

'Yan adawa na ci gaba da zanga zanga a Macedonia

Madugun ‘yan adawan kasar Macedonia Zoran Zaev ya lashi takobin ci gaba da jagorantar zanga zanaga a kan titunan kasar, har sai frainminista Nikola Gruevski na jam’iyyar conservative yayi murabus. Ana ci gaba gudanar da zanga zangar a cikin luman, sai dai jami’an tsaro sun dauki matakan dakile duk wani rikici da ka iya barkewa.Yayin da yake jawabi ga kimanin mutane dubu 20 da suka halarci zanga zagar a birnin Skopje, madugun ‘yan adawan kuma shugaban jam’iyyar SDSM Zoran Zaev, yace zasu ci gaba da zama a gaban gine ginen gwamnati, har sai Fraiminista Nikola Gruevski ya saki madafun ikon kasar.Masu zanga zangar sun yi ta daga tutoci, suna rera wakokin samun nasara.Gwamnatin kasar na fuskantar mummunan rikicin siyasa gami da tashe tashen hankula, lamarin da ya kara dagulewa a karshen makon da ya gabata, lokacin da aka kashe mutane 18 a wani harbe harben da aka yi tsakanin ‘yan sanda da ‘yan tawaye, ‘yan asalin kabilar Albaniya, a garin Kumanovo dake arwacin kasar.Wannan ne rikicin da ya fi kowanne muni a kasar, dake a matsayin daya daga cikin kasashe 5 na tsohuwar tarayyar Yugoslavia, tun bayan wanda ya faru a shekarar 2001, tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen na Albaniyawa. 

'Yan sandan kasar Macedonia suna sunturi
'Yan sandan kasar Macedonia suna sunturi REUTERS/Ognen Teofilovski
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.