Isa ga babban shafi
Faransa

Masu kyamar auren jinsi sun gudanar da zanga zanga a Paris

A yau lahadi dubun dubatar masu zanga zangar kin jinin dokar da ta halasta auren jinsi suka gudanar da zanga zangar neman soke dokar a Paris babban birnin kasar Fransa.

Zanga zangar kyamar halasta auren jinsi a birnin Paris
Zanga zangar kyamar halasta auren jinsi a birnin Paris REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Kafin wannan rana dai, wakilan majalisun dokokin kasar da dama sun sha yin kiran fasa gudanar da zanga zangar, wace suka danganta da bijere wa dokokin kasar. tare da nuna fargabarsu kan yiyuwar barkewar rikici a lokacin zanga zangar da aka gudanar cikin tsauraran matakan tsaro

A ranar 23 ga watan jiya ne majalisar dokokin kasar ta amince da dokar bayar da dama ga namiji ya aure namiji dan uwansa, mace kuma ta auri mace, har ma da ba su damar renon yaron da suka ki bin hanyar da ake samar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.