Isa ga babban shafi
Kotun Duniya-Kosovo

Kotun Duniya kan l;aifukan yaki a Yugoslavia, ta wanke tsohon Firaministan kasar

Kotun Majalisar Dinkin Duniya dake sauraren laifukan yakin da aka tafka a Yugoslavia, ta wanke tsohon Firaministan kasar, Ramush Haradinaj, tare da wasu ‘yan hanun damansa, daga zargin yin kisan gilla da azabtar da Serbiyawa, a lokacin rikicin kasar da aka tafka a shekarun 1990’

(Photo : Reuters)
Talla

Masu Shari’a a kotun ta Hague ne suka bayyana wanke tsohon Firaminista Ramush Hardinaj, daga zargin, inda suka bada iznin a yi maza-maza a sake shi.

A cewar Alkalan, laifukan da ake zargin tsohon Firaministan basu da tushe kana baza a iya dogaro da wasu bayanan da shaidun suka gabatar a gaban kotun ba.

A cewar daya daga cikin Alkalan, shaidar da daya daga cikin Shaidun ya bayar, na cewa ya kasance a cikin sansanin Jablanica, inda aka dinga azabtar da mutane tana da rauni, ya kuma kara da cewa, ta iya yiwuwa bashi labarin aka yi.

Haka zalika, kotun ta kara da cewa, koda an aikata zargin da ake yi akan tsohon Firaministan, babu kwakwarar shidar da ta nuna cewa Haradinaj, na sane da aika aika daya faru a sansanin na Jablanica
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.