Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta kwashe jami’anta da ke kasar Yemen

Kasar Amurka ta kwashe jami’anta daga kasar Yemen saboda abinda ta kira ci gaba da tabarbarewar tsaro a cikin kasar

Une série d'attentats meurtriers ont frappé des mosquées au Yémen ce vendredi matin à une heure de grande affluence des fidèles.
Une série d'attentats meurtriers ont frappé des mosquées au Yémen ce vendredi matin à une heure de grande affluence des fidèles. REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Babban jami’in Hukumar tsaron kasar Amurka Jeff Rathke, ya ce ya zuwa yanzu Amurka ta janye jami’anta daga kasar Yemen baki daya lura da harin baya-bayan nan da aka kaiwa Masallacin Jumu‘a da ya hallaka akalla mutane 150.

Wasu maharan da suka kira kansu 'ya'yan kungiyar ISIS ne suka kai wannan harin a babban Masallacin kasar ta Yemen inda aka bada labarin kwararar jini a Masallaci da kuma watsuwar Gawawwaki nan da can.

Tun bayan kai harin ne kuma kungiyar nan ta ISIS ta bayana daukar alhakin kai harin da kuma bata fito ta bayyana dalilin kai shi.

Baya ga harin Masallacin ma, akwai wani harin da aka kai a gidan adana kayan tarihi da ke a kasar ta Yemen

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.