Isa ga babban shafi
Yemen

An kai harin sama da Jirgi a fadar shugaban kasar Yemen

Jami’an tsaro a kasar Yemen, sun dauke shugaban kasar Abdulrabbu Mansur Hadi daga fadar gwamnati, tare da kai shi a wani wurin da za’a kula da shi, bayan da aka kai wani kazamin hari a fadar gwamnatin da ke a kudancin birnin Aden

Vikosi vya usalama vya Yemen vikiwa mbele ya ubalozi wa Ufaransa katika mji wa Sanaa, ambao ulifunga milango yake Februari 13 mwaka 2015.
Vikosi vya usalama vya Yemen vikiwa mbele ya ubalozi wa Ufaransa katika mji wa Sanaa, ambao ulifunga milango yake Februari 13 mwaka 2015. AFP PHOTO / MOHAMMED HUWAIS
Talla

Wani mai taimakawa shugaban kan sha’anin tsaro a kasar ya bayyana cewar an dauke shugaba Hadi ne zuwa wani wurin na daban, amma ba’a fitar da shi daga kasar ba.

Dazu da ranan nan ne aka ga wasu mutane a cikin Jirgin saman yaki da suka kai hari a fadar ta shugaban kasa ba zato ba tsammani, abin da ya haifar da barin Wuta daga Dakarun gwamnatin kasar da suka mai da martani.

Nan take dai Sojin kasar suka fito da dabarar dauke shugaban kasar daga fadar, suka kuma kai shi a wani wurin na daban a cikin sirri.

A watan da ya gabata ne dai Hadi ya samu mafaka a fadarsa da ke Aden bayan da ya gujewa yunkurin kamashi da ‘yan tawayen Huthi masu dauke da muggan makamai suka yi.

Ya zuwa yanzu dai fadan ya haddasa mutuwar akalla mutane 6 tare da jikkata fiye da 20, da kuma tilasta rufe Filin JIrgi a birnin na Aden.

Fadan dai ya barke ne tsakanin Dakarun gwamnati masu biyayya ga shuga Abdurrabu Masor Hadi, da na ‘yan tawayen Huthi.

Wadanda suka mutu din kuma, sun hada da Jami’an tsaro 3, da wasu mambobin wani kwamitin tsaro, kazalika da wasu mutane na daban.

Kasar Yemen mai kawance da Amurka dai ta fada cikin tashin hankali ne tun bayan da gwamnatin shugaba Ali Abdallah Saleh ta sauka a farko-farkon shekarar 2012.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.