Isa ga babban shafi
Yemen

Gwamnatin kasar Yemen ta ci gaba da mulki daga birnin Aden

Minister tsaron kasar Yemen ya kama aiki a sabon offishin sa dake birnin Aden, bayan ya sha da kyar a hannun mayakan Huthi a birnin Sanaa. Tuni shugaban kasa Abedrabbo Mansur Hadi ya umarci mukarabansa, dasu koma abirnin na Aden, don cigaba da aiki su har zuwa lokaci da za a kwato birnin Sanaa, dake karkashin ikon mayakan Huthi.Yanzu haka an kafa sabuwar fadar gwamnatin a birnin na Aden dake kasar Yemen, bayan shugaba Abedrabbo Hadi ya tsere daga hannu mayakan Huthi, da yanzu haka suke rike da fadar gwamnatin kasar.Shima Minister tsaron kasar Janar Mahmud Subaihi ya samu nasara tserewa, bayan wata musayar wuta da ‘yan tawayen, wandanda ke wa manyan jami’a gwamnati kasar daurin talala.Rahotanni dai na cewa Dogari daya ya rasa ransa yayin da yake kokarin kare lafiyar ministan, a lokacin da yake kokarin tserewa, kamar yadda jami’a tsaron kasar suka sanar. Dakarun kasar, sun kuma sanar da cewa mayakan sun cafke wasu mutane 5 dake cikin tawagar sa, yayyin da wata majiya ke cewa akalla mutane 12 ne suka rasa rayukan su.Yanzu haka dai akwai Fraiministan kasar, Khalid Bahab da wasu ministoci kasar, da fda ‘yan tawayen suka yiwa daurin talala a birnin Sanaa.Tun cikin watan Fabairu da ya gabata, mayakan na Huthi suka yi amfani da karfi wajen yin kane-kane a kan karagar mulki kasar bayan kora shugaban Hadi.Birnin Aden, gari na biyu mafi girma a kasar Yemen, ya kasance fadar gwamnatin kasar tun bayan samun ‘yancin kasar, kafin daga bisani aka koma Sanaa, da kuma yanzu ya fada hannun ‘yan tawaye. 

Shugaban kasar Yemen, Abdrabuh Mansur Hadi.
Shugaban kasar Yemen, Abdrabuh Mansur Hadi. AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.