Isa ga babban shafi
Yemen

Ban Ki-moon ya bukaci a dawo da Hadi kan madafan ikon Yemen

Sakararen Majalisar Duniya Duniya Ban Ki-moon ya yi kira a gaggauta dawo da Shugaban Yemen Abedrabbo Mansour Hadi kan madafan ikon kasar bayan mayakan Huthi sun hambarar da gwamnatin shi tare da rusa majalisa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon.
Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon. Photo/Eskinder Debebe
Talla

Ban Ki-moon da ke magana da manema labarai a Saudi Arebiya, ya ce ya zama wajibi a dawo da halataccen shugaba Hadi kan madafan ikon Yemen.

Ban ki Moon ya bayyana cewar halin da ake ciki a kasar ta Yemen na dada tabarbarewa saboda rashin gwamnati, sakamakon kwace mulkin da ‘Yan Tawayen Huthin suka yi.

Ban ya zargi ‘yan tawayen da kuma tsohon shugaban kasa Ali Abdallah Saleh a matsayin wadanda suke hana ruwa gudu a cikin kasar.

Kasashe shida na kungiyar hadin kan tekun Fasha sun bayyana abin da ‘yan tawayen suka yi a matsayin juyin mulki.

A ranar Juma’a ne dai Mayakan Huthi mabiya shi’a suka rusa gwamnatin Yemen bayan sun karbe ikon fadar shugaban kasa tare kame shugaba Hadi da ke samun goyon bayan kasashen yammaci.

Jekadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen Jamal Benomar ya yi kira ga bangaorirn siyasar kasar Yemen su hau teburin sasantawa bayan Mayakan huthi sun karbe gwamnati tare da rusa majalisa.

Jekdan yace suna fatar a yau Litinin bangarorin siyasar Yemen hadi da wakilan mayakan huthi za su hau teburin sulhu, bayan Ban-Ki-moon ya bukaci a dawo da shugaba Abedrabbo Mansour Hadi saman madafan iko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.