Isa ga babban shafi
Yemen

Mayakan Huthi sun kwace fadar Shugaban Yemen

Mayakan Huthi a Yemen sun kwace fadar Shugaban kasa tare da kai hari gidan shugaba Abdrabuh Mansur Hadi a wani mataki na kokarin hambarar da gwamnatinsa da ke samun goyon bayan kasashen yammaci. Yanzu haka kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa domin tattauna batun.

Sajoji a fadar Shugaban kasar Yemen a Sanaa
Sajoji a fadar Shugaban kasar Yemen a Sanaa REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Majalisar Dinkin Duniya ta yi allawadai da kwace fadar shugaban kasar da ‘Yan Tawayen suka yi a kasar tare da bayyana goyan bayan ga shugaba Abdrabuh Mansur Hadi.

Shugaban mayakan Abdul Malik al-Huthi, ya fito yana cewa suna adawa ne da gwamnatin Hadi tare da gargadin za su yi watsi da duk wani mataki da Majalisar Dinkin Duniya za ta tauka.

Rahotanni sun ce mayakan sun kai harin ne a gidan Shugaban kasa da ke yammacin birnin Sanaa fadar gwamnatin kasar, kuma sun kai harin ne a lokacin da shugaban kasar ke jagorantar taron tsaro da masu ba shi shawara.

Wasu sheadun gani da ido sun tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa mayakan na Shi’a sun kashe Sojoji guda biyu.

‘Yan tawayen sun dade suna iko da akasarin birnin Sanaa. Kuma Rahotanni sun ce sun harba makamin roka kan fadar shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.