Isa ga babban shafi

Mayakan 'yan Shi'a sun kwace wani sansanin sojan kasar Yemen

Mayaka ‘yan Shi’a sun bayyana kwace wani sansanin sojan kasar Yamen, wanda ke kusa da fadar Shugaban kasar dake birnin Sana’a. Mayakan sun bayyana hakan ne, bayan fafatawa da Dakarun gwamnatin kasar, lamarin da ya kai ga hasarar rayukan wasu mutane.Bayan anyi ta gwabza fada a babban birnin kasar ta Yemen wato Sanaa a yau Littini, ala tilas aka sanya hannu cikin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mayaka ‘yan Shi’a da kuma Dakarun Gwamnati.Wata majiya daga bangaren tsaron kasar ta tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar tsakanin bangarorin biyu, da kuma Ministan tsaro da Ministan Harkokin cikin gidan kasar.Mazauna harabar da fadar Shugaban kasar take sun gaskata cewa anji shiru bayan aman wuta da akayi a jiya, na tsawon sao’i da dama.Tun da safe yau litinin, kungiyar kasashen Larabawa ta roki bangarorin dake riici da juna, kan su tsagaita wuta ba tare da wani jinkiri ba.Mukaddashin Sakataren kungiyar Ahmed Bin Helly ne ya gabatar da bukatar kunhgiyar a wani taron manema labarai da aka yi a birnin Alkhahirar kasar Masar.Ya zuwa dazun nan dai ance rayukan mutane 2 suka salwanta, wasu 14 kuma na cikin. 

Wani gini dake cikin fadar shugaban kasar Yemen
Wani gini dake cikin fadar shugaban kasar Yemen REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.