Isa ga babban shafi
Yemen

Wani harin sama ya yi sanadiyyar mutuwar wani dan shugaban kungiyar al-Qaeda a Yemen

Wani hari da aka kai da jirgin sama marasa matuki a Yemen, ya yi sanadiyar mutuwar wani babban shugaban kungiyar Al –Qaeda a yau juma’a.A cewar wasu majiyoyi masu karfi an kai harin ne da sanyin safiyar yau Juma’a ta hanyar yin amfani da kuraman jirage ko kuma jirage marasa matuka.Lamarin ya yi sandiyar mutuwar Qaeed al-Dhahab, wanda jigo ne a kungiyar Al Qaeda a yankin na Yemen.Rahotanni na nuna cewa Al Dhahab, yana kan hanyarsa ne ta zuwa kauyen Manasseh dake kudancin gundumar Bayda a lokacin da aka kai hari akan motar da yake ciki, inda har ila yau wasu mutane biyu suka mutu.Yanzu haka akalla harin jirage marasa matuka goma aka kai a gabashi, da Kudancin Yemen wadanda suka kashe sama da mutane 40 tun daga watan Yulin wannan shekara zuwa yanzu.Ana dai zargin kasar Amurka ce ke kai hare haren ta yin amfani da ire-ire wadannan jirage. 

Daya daga cikin kuramen jiragen saman Amurka
Daya daga cikin kuramen jiragen saman Amurka
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.