Isa ga babban shafi
Yemen

Harin Masallacin Yemen ya munana

Ya zuwa yanzu yawan wadanda suka mutu sakamakon harin Bomb da aka kai a Masallacin birnin Sana’a na kasar Yemen ya kai 142

Un policier à la recherche d'indices sur le lieu de la première explosion, à Sanaa, le 20 mars 2015.
Un policier à la recherche d'indices sur le lieu de la première explosion, à Sanaa, le 20 mars 2015. REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Wani lokaci a jiya Jumu'a ne aka bayyana cewar kungiyar nan ta ISIS ta bayyana daukar alhakin kai harin da aka bayyana a matsayin mafi muni da aka kai a cikin kasar.

Wannan kuma shi ne karon farko da kungiyar ta dauki alhakin kai harin da aka ce an ga jinni yana ta malala a Masallaci, ga kuma gwawwakin mutane, abin dai babu kyaun gani.

A ranar Jumu’ar da ta gabata dai ne wasu mahara suka haka oma-Bomai a babban Masallacin birnin Sanaa, suka kuma tayar da su a daidai lokacin da ake Sallah, inda kai tsaye aka bada labarain mutuwar mutane sama da 30, mamatan kuma sai karuwa suke kama daga lokacin da harin ya auku zuwa yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.