Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

ICC za ta binciki laifukan Yaki da aka aikata akan Falasdinawa

Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC ta kaddamar da binciken aikata laifukan yaki akan Falasdianwa, matakin da kasar Isra’ila ke adawa da shi. Ofishin Fatou Bensouda babbar mai gabatar da kara a kotun ya ce zai gudanar da bincike akan ta’asar da Isra’ila ta aikata a Gaza.

Fatou Bom Bensouda Babbar mai gabatar da kara a kotun ICC
Fatou Bom Bensouda Babbar mai gabatar da kara a kotun ICC DR
Talla

Wannan matakin na zuwa ne bayan Falasdianwa sun samu wakilci a kotun domin kalubalantar Isra’ila.

Akalla Falasdinawa 2,200 suka mutu a hare haren da Isra’ila ta kai wa Falasdinawa a watan Afrilu, yayin da kuma aka kashe Sojojinta 73.

Firaministan Isra’ila ya yi watsi da matakin na kotu yana mai zargin Hamas da aikata laifukan yaki sabanin Isra’ila da ke kare kanta daga hare haren ‘Yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.