Isa ga babban shafi
Iran-Iraq-Amurka

Iran tace ba zata halarci taron da za yin kan Iraqi a Faransa ba

Iran tace ba zata halarci taron kasashen duniya da za a yi a kasar Faransa, inda za a duba yadda za a bullowa kungiya IS. Dama mahalarta taron sun ki gayyatar hukumomin na birnin Tehran, saboda rawar da ake zargi Iran na takawa a Syria da sauran kasashen duniya.Kasar ta Iran tace taron na yau Litinin ba zai yi wani tasiri ba, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, yace Iran din bata sha’awar shiga taron, da aka zabo wadanda ake so su halarta.Amir-Abdollahian yace abinda Iran ke fatan gani shine yaki da ta’addanci na gaske, a yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya, amma ba irin wannan yakin ba.Dama dai kasashen da suka shirya taron, basu gayyaci hukumomin na birnin Tehran ba, sakamon turjiyar da Amurka ta nuna kan gayyatar Iran din, saboda rawar da ake zargi tana takawa a kasar Syria.Amurka na ci gaba da nema hadin kan kasashen duniya, a kokarin da take yi na yakar kungiyar ta IS, kuma tace tana shirin kai hari ta sama kan mayakan dake yankunan kasar Syria, sai dai tace zata yi hakan ne ba tare da neman amincewa hukumomin kasar ta Syria ba. 

Jagoran addini na kasar Iran Ayatollh Ali Khameni tare da Shugaban kasa Hassan Rohani
Jagoran addini na kasar Iran Ayatollh Ali Khameni tare da Shugaban kasa Hassan Rohani مهر
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.