Isa ga babban shafi
Afghanistan-Amurka

Sojan Afghanistan ya bindige Janar na Sojan Amurka

Kasar Amurka ta tabbatar da kashe Harold Green Janar na Sojanta da ke aiki a kasar Afghanistan a karkashin kungiyar kawancen tsaro na NATO, bayan wani sojin Afghanistan ya bude masa wuta tare da wasu sojojin Britaniya da Afghanistan a Kabul.

Janar din Amurka da aka kashe a Afghanistan
Janar din Amurka da aka kashe a Afghanistan US Army
Talla

Mutane da dama ne Sojan ya jikkata ciki har da wani Janar na kasar Jamus.

Wannan shi ne babban Jami’in Sojan Amurka da aka kashe tun harin 11 ga watan Satumba a 2001.

Sojan na Afghanistan ya bude wuta ne a wani sansanin da dakarun Amurka ke bayar da horo ga Sojojin Afghanistan. Sai dai kuma shi kansa Sojan an kashe shi bayan ya bude wutar a lokacin da manyan kwamandojin kungiyar tsaro ta NATO suka kawo ziyara a sansanin.

Sojoji da dama ne Sojan na Afgahnsitan ya rauntana ciki har da wani babban Jami’in Sojan kasar Jamus.

Mahukuntan Afghanistan sun ce Sojan gona ne ya aikata ta’asar, tare da cewa ba lalle ba ne Sojan kasar Afghanistan ba ne.

Wannan al’amarin kuma yanzu ya kawo cikas ga tsarin bayar da horon da Amurka ke jagoranta, bayan ficewar dakarun kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.