Isa ga babban shafi
Afghanistan

Mayakan Afghanistan 800 sun kai hare hare a kudanci

Akalla mayakan Taliban 800 ne suka kai hare hare a Kudancin kasar a wani yunkuri na mallake wani yanki da dakarun kasar Amurka suka fice daga ciki, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fafaren hula 40 cikin kwanaki biyar.

Wani wuri da aka fafata tsakanin dakarun Afghanistan da mayakan Taliban
Wani wuri da aka fafata tsakanin dakarun Afghanistan da mayakan Taliban REUTERS/ Stringer
Talla

Sai dai bayanai na nuna cewa an kashe ‘yan kungiyar su kusan 100 a wannan hari, kamar yadda ma’aikatar ayyukan cikin gida ta sanar.

Rahotanni sun ce harin an kai shi ne a Gundumar Sangin, inda dakarun Amurka suka fice a watan da ya gabata.

Bayanai har ila yau na nuna cewa akalla dakarun kasar ta Afghanistan 21 sun rasa rayukansu a wannan arangama.

Kungiyar ta Taliban, ta jima tana tayar da kayar baya a kasar ta Afghanistan lamarin da ya lakume rayuka da dama a kasar ciki har da na fararen hula.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.