Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta kai mummunan hari a Kabul

Kungiyar Taliban a kasar Afghanistan ta kaddamar da wasu munanan hare hare a tashar jiragen saman birnin Kabul inda aka yi ta jin karar harbe harbe da fashe fashe. Jami’an tsaron kasar sun ce an shafe tsawon sa’o’I hudu ana barin wuta.

'Yan sandan Afghanistan sun fake suna barin wuta da Mayakan Taliban a Kabul
'Yan sandan Afghanistan sun fake suna barin wuta da Mayakan Taliban a Kabul REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO da sansaninta ke kusa da tashar jiragen ta yi amfani da jiragen sama wajen taimakawa sojojin Afghanistan fuskantar Yan bindigan. Janar Ayub Salangi, mataimakin ministan cikin gida yace dakarun sun yi nasarar murkushe ‘Yan bindigan cikin kankanin lokaci.

Jami’an tsaro sun ce sun yi nasarar kashe ‘Yan bindigar amma wani Jami’in tsaro ya samu mummunan rauni.

Tuni aka dakatar da sufurin jiragen sama zuwa tashar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.