Venezuela : Maduro ya kira taron gaggawa na kudancin Amurka
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bukaci kasashen yankin Kudancin Amurka da su kira taron gaggauwa domin tattauna rikicin siyasar da ake fama da shi a kasar.
Wallafawa ranar:
Kiran na shugaban Maduro na zuwa ne kwana daya bayan da ya kori jakadan kasar Panama da ke birnin Caracas, bayan da gwamnatin Panaman wadda ke da alaka ta kut da kut ta yi kira ga kasashen yankin su gudanar da wani taro domin daukar mataki akan gwamnatin kasar ta Venezuela mai fama fa tarzomar ‘yan adawa.
‘Yan adawa a kasar ta Venezuela suna nuna rashin gamsuwarsu ne akan irin kamun ludayin Maduro game da mulkin kasar wacce ke da arzikin man fetur bayan ya gaji Marigayi Hugo Chavez.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu