Isa ga babban shafi
Venezuela

Ɗalibai suna zanga-zanga a kasar Venezuela

Sama da Ɗalibai 2,000 ne suka fito saman titin birnin Caracas suna gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati, bayan an kashe wasu cikinsu mutane uku a jiya. Ɗaliban sun kaddamar da zanga-zangar ne domin adawa da tsadar rayuwa.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga masu Zanga-zanga a kasar Venezuela
'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga masu Zanga-zanga a kasar Venezuela REUTERS/Jorge Silva
Talla

Wannan ne babban ƙalubale da Shugaba Nicols Maduro ke fuskanta tun lokacin da ya gaji marigayi Hugo Chavez.

Tuni Maduro yace ba zai sauka daga muƙamin shugaban kasa ba inda Ƴan adawa ke neman ya yi murabus.

Henrique Capriles Babban mai adawa da gwamnatin Maduro yace al’ummar Venezuela sun fito ne suna neman canji a lokacin da ya ke mayar da martani bayan arangamar da aka yi tsakanin Ƴan adawa da masu goyon bayan gwamnati.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin Bil’adama sun yi kira ga gwamnatin Venezeula ta hukunta wadanda suke da hannu ga kisan mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.