Kotu ta umurci a sake duba na'urorin da aka yi zabe da su a Venezuela
A kasar Venezuela kurar siyasa ta dan lafa bayan da hukumar zaben kasar ta amince da sake binciken na’urorin da aka gudanar da zabe da su a kasar, amma ba za a sake kidaya kuri’un zaben shugabancin kasar da aka gudanar a kasar ba.
Wallafawa ranar:
A jiya juma’a 19 ga wannan wata ne shugaban kasar Nicolas Maduro ya yi rantsuwar soma aiki, bikin da ke da matukar muhimmanci a gare shi, inda yake sa ran ganin an samu raguwar yawan kasashen duniya da ke da shakku a kan zabensa a matsayin shugaban kasar ta Venezuela.
Shi dai Maduro, ya gaji marigayi Hugo Chavez ne mai ra’ayin gurguzu, to sai dai ‘yan adawa sun yi watsi da nasarar da aka ce ya samu a zaben, suna zargin cewa an tafka magudi ne kawai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu