Isa ga babban shafi
Venezuela

An kori ma'aikatan diflomasiyyar Amurka uku daga kasar Venezuela

Gwamnatin Venezuela ta umurnci wasu ma’aikatan diflomasiyyar Amurka uku da su bar kasar daga yau litinin bisa zargin jami’an da yin ganawa a asirce da wakilan kungiyar daliban kasar.

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro Reuters
Talla

Shugaba Nicolas Maduro ne ya bayar da wannan umurni, inda ya zargi Amurka da kokarin kifar da gwamnatinsa ta hanyar mara wa masu adawa da shi.

An dai share tsawon makwanni ana tarzomar nuna kin jinin gwamnatin shugaban, yayin da ake zargin sa gazawa wajen tunkarar matsaloli da suka hada da hauhawar farashin kayan abinci da rashin tsaro a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.