Isa ga babban shafi
MDD-Mali

China za ta tura sojoji zuwa kasar Mali

China tabi sahun sauran kasashen duniya, wajen aikewa da karin dakarunta, domin aikin samar da zaman lafiya a kasar Mali.Rahotanni daga Bamako sun ce China zata kai karin sojojin ta 245 zuwa Mali, bayan 150 da ta riga ta girke tun a watan Disamban da ya gabata a garin Gao, domin aikin samar da zaman lafiya.Wata majiya daga ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da aikin samar da zaman lafiya a Mali, ta tabbatar da kai karin sojojin, ba tare da bayani kan ko yaushe za’a kai su ba.Dakarun Majalisar Dinkin Duniya sun karbi akin samar da zaman lafiya a Mali tun a watan Yuli na bara, daga hannun takwarorin su na kungiyar kasahsen Afrika wadanda suka yi nasarar kubutar da Mali daga hannau ‘yan Tawaye tare da sojojin Faransa.Kasar Faransa na janye dakarun ta 5,000 dake cikin Mali, inda tace zata bar 1,000 kawai a cikin kasar. 

Wasu sojojin kasar China, da ke aiki a Mali
Wasu sojojin kasar China, da ke aiki a Mali Photos: MINUSMA/Fred Fath
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.