Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Dakarun Faransa sun kashe 'yan tawaye 10 a Mali

Kasar Faransa ta ce Dakarun ta sun kashe ‘yan tawaye 10 masu kishin Addini a kasar Mali.Dakarun kasar Faransa sun bayyana cewar akalla ‘yan tawaye masu kishin Addini 10 ne suka kashe sakamakon musayar Wuta da akayi tsakanin Dakarun kasar Faransa da ‘yan tawayen.Hukumomi a kasar Faransa ne suka tabbatar da wannan labarin inda suka bayyana cewar Dakarun ta sun fuskanci tsananin jajircewa daga ‘yan tawayen na Arewacin Mali, masu barazanar hana a gudanar da zaben da za’ayi a kasar a cikin Watan Nuwamban Bana.A cikin Watan Junairu dai ne kasar ta Faransa ta aike da Dakarunta a tsohuwar kasar da Faransa ta yiwa mulkin mallaka.Faransa dai tace ba zata rage yawan Dakarun ta daga Dubu Ukku da Dari Biyu, zuwa Dubu Daya ba, kamar yanda aka bukaceta da yi.Mai magana da Yawun Dakarun kasar ta Faransa na musamman masu fada da ‘yan tawaye, Gilles Jaron ya shaidawa manema labarai cewar suna da shirin rage Dakarun su zuwa Dubu Daya ne ya zuwa Watan Junairu, zuwa farkon Watan Fabrairu.Amma inji Jami’an kasar Faransa batun rage yawan Dakarun kasar ya dan jaa baya saboda zaben ‘yan Majalisar da za’a gudanar a ranar 24 ga Watan Nuwamba.Kasancewar Dakarun Faransa da na Majalisar Dinkin Duniya duka a Mali, basu hana kai jerin hare-hare da ake yi a kasar ba, inda mafi yawanci akan kai ire-iren wadannan hare-haren ne da manufar tarwatsa Dakarun kasar.Wannan Runduna ta musamman daga kasar Faransa dai ta yaki ‘yan ta’addan ne a ranar daya ga Watan Ocotoba, a wani kauye mai suna Douaya dake a Arewacin garin Timbuktu, bayan da suka samu Rahoton asiri na kokarin kai hari ga jami’an Sojin kasar. 

Sojojin Faransa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali
Sojojin Faransa da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali MALI-UN/ REUTERS/Joe Penney/Files
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.