Isa ga babban shafi

Mutane 35 ne suka mutu a wani hatsari tsakanin wata motar bas da motoci a Masar

Wani mummunan karo da aka yi a hanyar Hamadar Alkahira zuwa Alexandria kusa da Wadi al-Natrun ya yi sanadiyar mutuwar mutane 35, akalla 18 daga cikinsu sun kone kurmus," in ji shafin yada labarai na Al-Ahram, wanda ke nuni da "akalla 53 sun jikkata"

Hatsarin mota
Hatsarin mota REUTERS - STRINGER
Talla

Kafafen yada labaran kasar sun bayyana cewa  hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar "mutane 35, akalla 18 daga cikinsu sun kone.

Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wata motar daukar kaya da ta fadi a kan babban  titin ta kuma kone.

Na kuma hango akalla bas guda daya da karamar bas, dukkansu da wuta ta kone, da kuma motoci da dama, wasu kuma suna ci da wuta.

Hatsarin mota
Hatsarin mota REUTERS

Ana iya ganin cunkoson jama'a a tsaye a gefen titin, suna kallon wurin da hatsarin ya afku, tare da layukan motoci, yayin da hayaki mai kauri ya turnuke sama.

Hatsarin mota ya zama ruwan dare a kasar Masar inda galibin babu kulawa da ta dace a tituna kuma ana yin watsi da ka'idojin hanya.

Wani hatsarin mota a Senegal
Wani hatsarin mota a Senegal © Ousseynou Diop/AFP

Alkaluman hukuma sun ce mutane 7,000 ne suka mutu a hatsarin mota a shekarar 2021 a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a kasashen Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.