Isa ga babban shafi

Manyan motoci dauke da kayayyakin agaji sun shiga Gaza a karon farko

Rukunin farko na manyan motocin dakon kaya dauke da kayayyakin agaji ya shiga yankin Zirin Gaza wanda ke fama da hare-haren Isra’ila ta mashigar Rafah daga Masar a Asabar din nan.

Manyan motocin dakon kaya na kungiyar  agaji ta Red Crecent dauke da kayayyakin jinkai zuwa Zirin Gaza daga Rafah Asabar 21 ga Oktoba.(AP Photo/Mohammed Asad).
Manyan motocin dakon kaya na kungiyar agaji ta Red Crecent dauke da kayayyakin jinkai zuwa Zirin Gaza daga Rafah Asabar 21 ga Oktoba.(AP Photo/Mohammed Asad). AP - Mohammed Asad
Talla

Wannan ne karon farko da motoci masu dauke da kayayyakin agaji suka shiga Gaza tun da wannan yaki ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas, mai mulkin Gaza, sama da makwanni biyu da suka wuce.

Kasashen duniya sun fara tsokaci a game da wannan al’amari na kokarin isar da agaji ga wannan yanki da yaki ya daidaita, inda shugaban hukumar kula da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce yana da kwarin gwiwar cewa wannan ne masomin ci gaba da shigar da kayayyakin agaji ga al’ummar Gaza.

Mashigar Rafah dai ita ce hanya daya tilo ta shiga Zirin Gaza,  wadda ba a hannun Isra’ila take ba,  kuma kasar ta Yahudawa ce ta  amince a  shigar da agaji ta hanyar, biyo bayan bukatar hakan daga babbar  aminiyarta, Amurka.

Isra’ila tana luguden wuta a kan Zirin Gaza tun bayan harin da  mayakan Hamas suka shammace ta da shi a ranar 7 ga watan Oktoba; hakan ya sa Isra’ilar ta ayyana yi wa yankin kawanya, inda ta yanke wutar lantarki da ruwa da makamashi.

Tun daga lokacin da aka fara kai wadannan hare-haren, sama da  Falasdinawa dubu 4 da dari 1 ne suka mutu, akasarin su fararen hula, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Hamas ta sanar.

An rufe wannan mashiga ta Rafah bayan da wadannan motocin dakon kaya  20 suka wuce da kayayyakin agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.