Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen duniya na taron zaman lafiya kan Gaza a Masar

A Asabar din nan ne ake  sa ran Masar ta karbi bakuncin shugabannin kasashen duniya don gudanar da taron zaman lafiya, a don tattaauna rikicin da ake yi yanzu haka tsakanin Israa'ila da kungiyar Hamas ta yankin Falasdinu.

Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi, wanda zai karbi bakuncin taron zaman lafiya a kan Gaza.
Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi, wanda zai karbi bakuncin taron zaman lafiya a kan Gaza. AFP - MICHAEL KAPPELER
Talla

 

 Taron ya mayar da hankali wajen samar da mafita ta dindindin kan rikicin da ke faruwa yanzu haka tsakanin Hamas da Isra’ila wanda ya hallaka  fararen hula fiye da dubu 4. 

Shugaban Masar Abdel Fattah Al-sisi shi ne mai masaukin baki a wajen taron da shugaban Falasdinawa mahomud Abbas da sauran shugabannin kasashen Larabawa irin su sarkin Jordan  Abdul’aziz, sai sarkin Bahrain Hamad Bin Isa Al Khalifa, da kuma Yarima mai jiran gadon masarautar Kuwait Sheikh Meshal al-Ahmad al-Sabah ke halarta.

Haka kuma taron yai halartar  Ministar harkokin wajen Japan Yoko Kamikawa da kuma ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna, da shugaban majalisar zartaswar Turai. 

Sauran shugabannin da halartar wanna taro sun hada da shugaban diplomasiyyar Turai Joseph Borell da sauran su. 

Ana iya cewa rikicin baya-bayan nan da ya barke tsakanin Hamas da Falasdinu ya janyo hankalin duniya, hakan ya sa ta ke  kokarin ganin ta samar da mafita ta karshe don takaita  fararel hular da ke mutuwa ba ji ba gani. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.