Isa ga babban shafi

Human Right Watch ta zargi Amurka da kawayenta da taimaka wa laifukan yaki a Gaza

Yayin da Falasdinawa da yaki ya daidaita a Gaza ke jiran agajin gaggawa da zai shigo ta kasar Masar, Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a yankin da Hamas ke iko da shi.

Wasu gine-gine da suka fuskanci hare-haren Isra'ila a yankin Gaza. 10/10/2023.
Wasu gine-gine da suka fuskanci hare-haren Isra'ila a yankin Gaza. 10/10/2023. AP - Fatima Shbair
Talla

Ma'aikatar harkokin cikin gida da Hamas ke iko da ita ta sanar da cewa, Isra’ila ta kai hare-hare wurare da dama ciki harda wani coci da wasu mutanen da suka rasa matsugunansu ke neman mafaka, inda akalla mutane 8 suka mutu wasu da dama suka jikkata.

Wasu da harin Isra'ila ya rutsa da su a Gaza.19/10/23
Wasu da harin Isra'ila ya rutsa da su a Gaza.19/10/23 AP - Fatima Shbair

Kazalika, wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a garin Khan Younis da ke kudancin Gaza ya kashe mutane akalla 21 tare da jikkata wasu da dama. An kuma kai munanan hare-hare a wasu yankunan Falasdinu.

Dole Isra'ila na samu nasara - Biden

Shugaba Joe Biden ya bayyana goyon baya ga Isra’ila a matsayin abu mai matukar muhimmanci ga tsaron kasar Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden. 19/10/23
Shugaban Amurka Joe Biden. 19/10/23 © Jonathan Ernst / AP

Yayin wani jawabi da ba kasafai ba a ofishin sa, shugaba Biden wanda ke shirin mika bukatar neman biliyoyin daloli domin taimakawa yake-yaken Isra’ila da Ukraine, ya ce, dole sai Isra’ila da Ukraine sun yi nasara a yakin da suke gwabzawa.

Human Right ta zargi Amurka da kawayenta

Tuni Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi Amurka da kawayenta na Turai da munafurci saboda gazawar su wajen yin Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza.

Gawarwakin wasu Falasdiwa da harin Isra'ila ya hakka a wani asibi dake zirin Gaza.17/10/23
Gawarwakin wasu Falasdiwa da harin Isra'ila ya hakka a wani asibi dake zirin Gaza.17/10/23 AP - Abed Khaled

Mataimakin daraktan HRW Tom Porteous ya ce, sabanin yadda Amurka da Turai suka yi wa Rasha tir kan mamayarta a Ukraine, amma suka yi shiru kan laifukan yaki da Isra'ila ke aikata wa a zirin Gaza.

Kayan agaji

Yanzu haka ana dakon kayan agaji ya fara isa Gaza ta Rafah da ke iyaka da kasar Masar, bayan da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da kulla yarjejeniya da Masar da Isra'ila don ba da damar shigar da kayan agajin jin kai a yankin da aka yi wa kawanya.

Motoci dauke da kayan agaji a kan iyakar Masar da Gaza.17/10/23
Motoci dauke da kayan agaji a kan iyakar Masar da Gaza.17/10/23 REUTERS - STRINGER

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya amince da cewa za’a bar manyan motoci 20 su fara shiga" yankin zirin Gaza da aka yi ruwan bama-bamai tun daga ranar Juma'a, tare da bai wa hukumomi lokaci domin gyara hanyoyi.

Adadin wadanda aka kashe a yankin Faladinawa

Kawo yanzu, adadin wadanda suka mutu a Gaza ya karu zuwa 3,785 tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Gaza ta sanar a ranar Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.