Isa ga babban shafi

Faransa da Masar na wani sabon ƴunkurin samar da tsagaita wuta a yakin Gaza

Ministan harkokin wajen Masar Sameh Shoukry ya gana da takwaran sa na Faransa kan yadda za’a tsagaita wuta a Zirin Gaza don kawo karshen zubar da jinin Falasdinu da Isra’ila ke yi.

Yadda World Central Kitchen ta fara raba abinci bayan kungiyar agajin ta koma aiki, a wata makaranta da ke dauke da mutanen da suka rasa matsugunnai, a Deir Al-Balah, tsakiyar zirin Gaza. 01/05/24
Yadda World Central Kitchen ta fara raba abinci bayan kungiyar agajin ta koma aiki, a wata makaranta da ke dauke da mutanen da suka rasa matsugunnai, a Deir Al-Balah, tsakiyar zirin Gaza. 01/05/24 REUTERS - RAMADAN ABED
Talla

Ziyarar da ministan harkokin wajen Faransa Stephane Sejourne ya kai birnin Alkahira, na zuwa ne bayan ganawar wakilan Amurka da Masar da kuma Qatar a a farkon makon nan, inda Isra’ila ta gabatrwa kungiyar Hamas tayin kulla yarjejeniyar tsagaita wutar kwanaki 40.

Har zuwa lokacn nadar wannan rahoto mayakan na Hamas na Nazari kan tayi yarjejeniyar wadda ta kunshi musayar fursunoni tskaninsu da Isra’ila kusan watanni bakwai bayan barkewar yaki a Zirin Gaza.

Shugaban Hamas Suhail al-Hindi ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, nan ba da jimawa ba zasu bayyana matsayar su kan wannan batu.

Hakazalika mahukuntan Isra’ila sun shaidawa AFP cewa, suna kan tattaunawa da kuma jiran amsoshin ko za su tura wakilan su zuwa wurin tattaunawar a Cairo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.