Isa ga babban shafi
Burundi

Alkalin kotun kolin Burundi ya gudu ya bar kasar.

A kasar Burundi ‘yan Sanda na ci gaba da gwabza fada da masu adawa da yunkurin Shugaba Pierre Nkuruziza na zarcewa kan karagar mulkin kasar.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga  a Burundi don nuna rashin amincewarsu da zarcewar Shugaba Nkurunziza
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Burundi don nuna rashin amincewarsu da zarcewar Shugaba Nkurunziza REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

 

Kafin wayewar gari yau Talata dai bayanai na nuna cewa ‘yan sandan kasar sun kashe mutane 13,
Mako daya kenan da fara bore , kamar yadda Pierre-Claver Mbonimpa na kungiyar kare hakkin biladama akasar ya gaskata.

Daga cikin mamatan 13 akwai soja daya da yan sanda biyu, bayaga tarin wadanda suka sami raunuka.

Tun lokacin da jam’iyyar dake mulki ta ayyana Shugaban kasar da cewa shine kadai taga ya dace ya zarce da mulki, mutanen kasar suka fara fito na fito, da hukuma.

Koda ajiya Sakataren wajen na Amirka John Kerry dake rangadi a Kenya ya tabo batun Burundi inda yake cewa bai dace ba shugaban kasar ya zarce bayan ya kamala wa’adinsa na biyu kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tsara.

Babban Alkalin kotun kolin kasar Burundi Sylvere Nimpagaritse da ake saran zai yanke hukunci kan halarcin tsayawa takarar shugaban kasar Pierre Nkurunziza na wa’adi na uku ya gudu ya bar kasar.

Alkalin ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Faransa cewar alkalan kotun 7 na fuskantar barazana daga bangaren gwamnati ciki har da barazana ga rayukan su dan amincewa da halarcin takarar Nkurunziza.

Sylvere yace akasarin alkalan sun amince cewar shugaba Nkurinziza bashi da hurumin tsayawa takara.

A ranar 26 ga watan gobe ne dai za a gudanar da babban zaben kasar a Burundi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.