Isa ga babban shafi

Karin kafofin yada labaran yammacin Turai sun fuskanci dakatarwa a Burkina Faso

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta ci gaba da dakatar da tarin kafofin yada labarai na ciki da wajen nahiyar Afrika, galibin wadanda suka wallafa labari kan rahoton kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch da ya bankado yadda Sojojin kasar suka yi wa tarin fararen hula kisan gilla.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan. © AFP
Talla

Tarin kafofin yada labarai na yammacin Turai ciki har da BBC Afrika da tawagar tashoshin TV5Mondes da kuma Voice of America su ke a sahun farko na jerin kafofin da suka fuskanci wannan dakatarwa daga mahukuntan na Burkina Faso wadanda gwamnatin Sojin ta zarga da wallafa labaran ƙage kan rahoton da kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta fitar da ke zargin Sojin kasar da kashe fararen hula akalla 223 a karkashin yakin da ta ke da fararen hular da ke tallafawa ‘yan ta’adda a sassan kasar.

Sashen yada labarai na gwamnatin Sojin ta Burkina Faso ya ce gungun tashoshin yada labarai mallakin Faransa na TV5Monde za su dakatar da ayyukansu na tsawon makwanni 2 a sassan kasar yayinda za a kulle shafin wallafa labaransu sai abin da hali ya yi.

Sauran kafofin labaran da wannan dakatarwa ta shafa sun kunshi sashen labarai mallakin Jamus na Deutsche Welle da jaridar Le Monde ta Faransa baya ga Ouest-France sai kuma Guardian ta Birtaniya sannan kamfanin dillancin labarai na Afrika APA da kuma Ecofin, wadanda dukkaninsu gwamnatin ta Burkina Faso ta dakatar da aikinsu ba tare da sanar da lokacin dawowarsu ba.

A karshen makon nan ne kakakin gwamnatin ta Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo ya yi watsi da rahoton na Human Right Watch wanda ya bayyana da tsantsar kage ga gwamnatin Sojin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.