Burundi ta yi watsi da zargin bude wuta ga masu zanga zanga
Gwamnatin kasar Burundi ta yi watsi da zargin da ake mata na cewa jami’an tsaro sun budewa masu zanga zanga wuta a wani fito na fito da ‘yan sanda kan matakin sake tsayawa takarar Shugabancni kasar na Shugaba Pierre Nkuruziza
Wallafawa ranar:
Ministan cikin gidan kasar ta Burundi Gabriel Nizigama ya shaidawa taron manema labarai cewa, a hukumance, jami’an tsaro a za su yi aiki da doka domin dakile duk wata zanga zanga da za a gudanar ba bisa ka’ida ba.
Nizigama ya kara da cewa, kawo yanzu bai samu bayani ba na cewar jami’an tsaro sun yi amfani da makamai domin tarwatsa ma su zanga zanga.
Ya kuma jaddada matsayin Burundi wajan kula da doka, inda ya siffanta ta da kasa mai aiki da doka da oda, kuma ya ja hanklulan al-umma cewa a horon da aka baiwa jami’an tsaron babu ta yadda za su bada goyan baya a tarzomar da za ta kai ga kashe fararen hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu