Isa ga babban shafi
Burundi

Amurka ta tura Jami'inta Burundi saboda rikicin siyasa

Kasar Amurka ta tura wani babban jami’in diflomasiyarta zuwa Burundi dan ganawa da hukumomin kasar kan tashin hankalin da ake samu kan shirin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na neman wa’adi na uku, sabanin kundin tsarin mulkin kasar

Wasu daga cikin masu zanga-zanga  a Burundi don nuna rashin amincewarsu da zarcewar Shugaba Nkurunziza
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a Burundi don nuna rashin amincewarsu da zarcewar Shugaba Nkurunziza REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Tom Malinowski, mataimakin Sakataren harkokin wajen kasar dake sa ido kan harkokin demokradiya, kare hakkin Bil-Adama da kuma yan kwadago, ya shaidawa manema labarai cewar yana hanyar zuwa Burundi dan ganawa da bangarorin siyasar kasar, dan ganin sun cigaba da bin tafarkin demokiradiya ba tare da samun tashin hankali ba.

Rahotanni sun ce akalla mutane 25,000 suka tsere daga kasar dan kaucewa tahsin hankali.

A dayan bangaren kuwa, Kotun kasar ta Burumdi za ta duba yiwuwar tsayawa takarar Nkurunziza kamar yadda majalisar dattawan kasar ta sanar.

Majalisar ta shaidawa kamfanin dillacin labaran faransa na AFP cewa, ta gabatar da batun ga kotun, inda ta neme ta da ta sa baki cikin lamarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.