Isa ga babban shafi
Burundi

Mutanen Burundi 21,000 sun tsallaka Rwanda

Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen kasar Burundi sama da 5,000 sun tsere zuwa kasar Rwanda tsakanin Assabar zuwa Lahadi saboda fargabar rikicin siyasa a cikin kasar. Yanzu adadin mutane 21,000 suka tsallaka zuwa Rwanda

Ana ci gaba da zanga-zanga a Burundi
Ana ci gaba da zanga-zanga a Burundi REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Hukumar kula da ‘Yan gudun hijira ta ce mutanen na Burundi na ci gaba da kwarara zuwa Rwanda a yayin da aka shafe kwanaki uku ana zanga-zangar adawa da matakin shugaban kasa Nkurunziza na neman wa’adi na uku akan madafan iko.

Akalla mutane biyar suka mutu a arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da ‘Yan sanda.

Rahotanni a yau Talata daga Bujunbura babban birnin kasar ta Burundi na cewa ‘Yan sanda na ci gaba da arangama da ‘Yan sanda.

Zanga-zangar dai ta barke ne a Burundi a ranar Lahadi bayan Jam’iyyar CNDD mai mulki ta ba shugaban kasa Pierre Nkurunziza damar neman wa’adi na uku a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 26 ga watan Yuni.

Kuma tun a 2005 ne shugaban ke jagorantar kasar, yayin da ‘yan adawa ke bayyana cewa matakin tazarcen ya sabawa kundin tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.