Isa ga babban shafi
Nijeriya,Bauchi

An harbi wani matashi mai zaman a kasa a tsare a Bauchi

Rahotanni daga garin Bauchi a Tarayyar Najeriya na cewa an harbi wani matashi da ke cikin dubban mutane ma su zaman dirshan a harabar ofishin hukumar zaben jihar tun daren jiya, inda suke neman lallai a bayyana sakamakon zabubbukan da aka gudanar.

Jami'an Tsaron Najeriya na aikin tsaro domin dakile barazanar Boko Haram
Jami'an Tsaron Najeriya na aikin tsaro domin dakile barazanar Boko Haram
Talla

Tun a daren jiya aka datse hanyar shiga wannan hukumar da zaman dirshin, hudubar ‘a kasa, a tsare ‘ har zuwa lokacin bayyana sakamakon zabe.

Mutanen da suka yi cuncurundo a ofishin sun bayyana wa wakilinmu Shehu Saulawa cewa ‘Babu wanda ya isa ya wuce kuma babu inda za su motsa har sai an sanar da sakamako’. sun kuma bayyana cewa akwai wani Jami’in Soji da ya bude mu su wuta, lamarin da ya yi ajalin wani matashi

Rahotannin dai na cewa karar harbin bindigogi a kewayan hukumar zaben ta jihar ya kara jefa fargaba da zullumi ga ma’aikatan Hukumar wadanda ke ci gaba da lissafin alkalluma Kuri’u.

Kakakin Hukumar Malam Aliyu Abubakar ya shaidawa Shehu Saulawa cewa suna gudanar da aikinsu cikin fargaba, saboda jami’an hukumar da kyar suke iya shiga offishinsu.

Malam Aliyu ya kuma ce suna jira a gama harhada sakamakon sauran kananan hukumomin Jihar kafin su sanar.

Wakilinmu Shehu Saulawa ya ce da alama dokar hannan zirga-zirga da aka sanya a cikin jihar tun a jiya ba ta yi wani tasiri ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.