Isa ga babban shafi
Turai-Ebola

Ma'aikatan sa kai daga Britaniya zasu kai dauki a Saliyo don yaki da Ebola

Yau Lahadi ake sa rai ayarin farko na masu aikin sa kai a bangaren lafiyan kasar Britaniya zasu isa kasar Saliyo, don taimakawa wajen yaki da cutar Ebola. Da yammacin jiya Asabar jami’an su fiye da 30, da suka hada da Lilkitoci, da sauran ma’aikatan kula da lafiya, suka tashi daga filin jirgin saman Heathrow na birnin London.Ana sa rai za a basu horaswa ta mako guda a birnin Freetown, kafin su watsu zuwa cibiyoyin jinya da hukumomin Britaniya suka giggina a kasar, dake yankin yammacin Africa, don kula da marasa lafiya. 

Wasu ma'aikatan lafiya dake yaki da cutar Eboal
Wasu ma'aikatan lafiya dake yaki da cutar Eboal REUTERS/U.S
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.