Isa ga babban shafi
Ebola

Ebola ta kashe mutane 4,960-WHO

Hukumar lafiya ta duniya, WHO tace adadin mutanen da suka mutu sakmakon cutar Ebola sun kai kimanin 4,960, kuma yanzu mutane kimanin 13,268 ke dauke da cutar a kasashe 8 masu fama da Ebola. Hukumar ta Lafiya tace adadin na iya zarce haka saboda yanayin yadda cutar ke yaduwa a yanzu da kusan kashi 70.

Jami'an kiwon lafiya suna fama da masu cutar Ebola a Waterloo, birnin Freetown a Saliyo.
Jami'an kiwon lafiya suna fama da masu cutar Ebola a Waterloo, birnin Freetown a Saliyo. REUTERS/Josephus Olu-Mamma
Talla

Kasashen Liberia da Guinea da Saliyo ne dai cutar ta fi yin kisa. Inda a Liberia aka samu mutuwar mutane 2,766 cikin mutane 6,619 da ke dauke da cutar.

A kasar Saliyo kuma mutane 1,130 ne suka mutu, yayin da a Guinea aka samu mutuwar mutane 1,054 da suka mutu sakamakon Ebola.

Najeriya da Senegal sun yi nasarar kawar da cutar, amma a Najeriya an samu mutuwar mutane 8 daga cikin mutune 20 da suka kamu da cutar. Kasar Senegal kuma mutum guda ne ke dauke da ita.

A kasar Mali ma an samu mutuwar wata yarinya mai shekaru biyu da ta shigo da cutar daga kasar Guinea. Haka ma cutar Ebola ta tsallaka zuwa Spain da Amurka.

Hukumar Lafiya ta duniya tace Jami’an kiwon lafiya 549 ne suka kamu da cutar, inda kuma aka samu mutuwar 311 daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.