Isa ga babban shafi
Somalia

Ana zargin sojojin wanzar da zaman lafiya da yiwa mata fyade a Somaliya

Wani Rahoton da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch ta fitar, ya bayyana yadda gamayyar sojojin kasashen duniya da aka tura aikin kwantar da tarzoma a yankin da ke fama da tashe tashen hankula a kasar Somaliya, suka shiga yiwa Mata da kananan yara ‘yan kasa da shekaru 12 fyade.Kungiyar dai ta ce wannan halin na matsayin keta hakkin bil’adama.Kungiyar ta ce baya ga dabi’ar yiwa matan fyade da karfin tsiya da Sojin ke yi, Sojojin suna hanawa duk matar da bata bada kanta ba abinci.Rahoton yace, daga cikin wadanda ake yiwa fyaden akwai iyaye mata da kuma ‘ya’yansu, harma da wadanda basu zarta shekaru 12 ba.Wasu daga cikin matan da ake yiwa fyaden, sun bayyana cewar Sojojin kan rudesu ne da Kudi, wani zubin kuma abinci, wadda ta ki kuma a kamata da karfin tsiya.Amma a nata bangaren rundunar Sojin ta karyata rahoton, harma tana bayyana shi a matsayin wanda babu adalci a ciki.Su dai wadannan dakarun Soji dubu 22, da aka debo daga kasashe 6 na Nahiyar Africa, na fada ne da ’yan kungiyar al-Shabab tare da dakarun gwamnatin kasar Somaliya.Akasarin matan da suka fada cikin wannan matsalar dai sun fito ne daga babban birnin kasar wato Mogadishu, da kuma wadanda suka gudo daga kauyuka sakamakon yunwar da aka yi fam ada ita a kasar cikin shekarar 2011. 

Wasu sojojin wanzar da zaman lafiya a Somaliya
Wasu sojojin wanzar da zaman lafiya a Somaliya Photo: Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.