Isa ga babban shafi
Somaliya

AU za ta kara dakaru a Somaliya

KWAMITIN Tsaro da wanzar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Africa, na shirin kara yawan dakarun samar da zaman lafiya a kasar Somalia, mai fama da tashin hankali. Kwamishinan tsaro na kungiyar, Ramtame Lamamra, yace matakin ya zama wajibi, ganin yadda tashin hankalin da ake cigaba da samu a Somalia, ke neman tsallakawa zuwa wasu kasashen Yankin.Matakin kara yawan dakaru na zuwa ne a dai dai lokacin da kasdar Kenya tayi tayin bada dakarun ta, ta kuma bukaci taimakon kasashen Amurka da Isra’ila, dan dakile aiyukan kungiyar Al Shabaab.Wani taro da shugabanin kasashen Kenya, Uganda da Somalia suka gudanar, ya sake bayyanaa kudirin kasashen nasu, na cigaba da yakar kungiyar, wanda ke kashe mutane baji ba gani.Dakarun kungiyar kasashen Afrika da na Majalisar Dinkin Duniya, sun yi nasarar korar kungiyar Al Shabaab daga birnin Mogadishu. 

Wasu mayaka Al Shabaab
Wasu mayaka Al Shabaab Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.