Isa ga babban shafi
Ebola

MDD za ta ciyar da mutane milyan 1 a inda ake fama da Ebola

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta ciyar da akalla mutane milyan daya a kasashen da ke fama da cutar Ebola.

Likita na binciken cutar Ebola
Likita na binciken cutar Ebola Reuters/Mariana Bazo
Talla

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar bayar da agaji ta Medecins Sans Frontiers ke cewa taimakon da kasashen duniya ke bayarwa domin yaki da cutar ya yi kadan, inda aka yi la’akari da yadda cutar ke saurin yaduwa.

Gargadin da kungiyar ta Medecins Sans Frontiers ta fitar a wannan juma’a, na nuni da cewa da farko kasashen duniya ba za su zaci cutar za ta iya yaduwa a cikin gaggawa zuwa sauran kasashe ba kamar dai yadda lamarin ke tafiya a yau ba.

Shugaban kungiyar wadda ta shahra wajen ba da agajin kiwon lafiya a duk inda bala’i ya bulla a duniya Joanne Liu, ya ce ba ya zaton cewa kokarin da kasashe a yanzu zai dakatar da yaduwar cutar a kasa da watanni shida masu zuwa.

To sai dai ofishin Hukumar abinci ta MDD a birnin Dakar wanda ke kula da yankin yammacin Afirka, a yau ya ce zai ciyar da mutane akalla milyan daya a kasashen Sierra Leone, Liberia da kuma Guinea Conakry da yanzu haka cutar ta kashe dimbin jama’a sannan ta hana gudanar da harkokin kasuwanci da dai sauransu.

Matakin na hukumar abinci, na a matsayin karba kiran hukumar lafiya ta duniya ne, wadda ta ce akwai mutane akalla milyan daya da aka killace a wadannan kasashe kuma dole ne sai an taimaka masu da abinci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.