Ebola: Gaisuwa ta fara wahala a Najeriya
A Najeriya, yanzu haka hankulan jama’a sun yi matukar tashi sakamakon yadda cutar nan ta Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu, yayin da wasu fiye da dari daya ke ci gaba da kasancewa a karkashin kulawar jami’an kiwon lafiya. A game da yadda cutar ke saurin yaduwa a tsakanin al’umma, wannan ya sa jama’a suka soma nuna kyama ta fanni cudanya ko kuma yin mu’amala a tsakaninsu. Wakilinmu na birnin Kano Abubakar Isa Dandago ya aiko da rahoto.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahoto: Mu'amula ta fara wahala a Kano
Hukumar lafiya ta duniya WHO tace girman Cutar Ebola da ke bazuwa a yammacin Afrika ya zarce tunanin mutane tare da kiran daukar matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar da ta kashe mutane 1,069.
Hukumomin Najeriya sun gana da jami’an hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya kan annobar cutar Ebola da yanzu haka ta kashe mutane 3 a cikin kasar. Daga Abuja Muhammed Kabir Yusuf ya aiko da Rahoto.
Rahoton Kabiru Yusuf daga Abuja akan Ebola
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu