Isa ga babban shafi
Najeriya

Ebola: Jami’ar Lafiya ta tsere Lagos

Rahotanni a Najeriya sun ce wata malamar jinyar da aka killace sakamakon mu’amala da mutumin kasar Liberia wanda ya mutu sakamakon cutar Ebola, ta fice daga birnin Lagos bayan hukumomin lafiya a kasar sun hana masu cutar su bar inda suke don kaucewa bazuwar Cutar.

Jami'an lafiya suna gudanar da bincike
Jami'an lafiya suna gudanar da bincike Reuters/Mariana Bazo
Talla

Ministan yada labarun kasar Labaran Maku yace Jami’ar Lafiyar din da ta kula da mutumin daya kai cutar Nigeria, da kuma ake sa ido a kanta, ta bar birnin Lagos a kudu maso yammacin kasar zuwa Jihar Enugu da ke a yankin kudu maso gabashi.

Ministan yace yazu ana sa ido kan mutane 20 da suka yi mu’amula da Jami’ar Lafiyar kai tsaye, da suka hada da mijinta.

Mr Maku yace yanzu akwai mutane kusan 200, da ake tunanin zasu iya kamuwa da cutar ta Ebola a kasar, da suka hada da wadanda ke jihar ta Enugu.
Har yanzu ba a tabbatar da kamuwar ko mutum daya ba a wata Jiha sabanin jihar Lagos da aka samu bullar cutar a Najeriya.

Zuwa yanzu cutar ta Ebola ta yi sanadiyar kisan mutane sama da 1,000, tun farkon wannan shekarar a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo. Najeriya, ce kasa ta 4 da cutar ta isa, kuma an tabbatar da kamuwar mutane 10, inda 3 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.