Isa ga babban shafi
Libya

Kasashen Yammaci sun bukaci ‘Yan kasarsu su fice libya

Kasashen yammacin duniya da dama sun bukaci ‘Yan kasarsu su fice daga kasar Libya saboda kazancewar rikicin kasar da ya lukume rayukan mutane kusan 100 a makwanni biyu da aka kwashe mayakan sa-kai na kai wa juna hare hare a birnin Tripoli.

Hayaki ya turmuke sama a kan hanyar Tashar jirgin sama a birnin Tripoli na Libya
Hayaki ya turmuke sama a kan hanyar Tashar jirgin sama a birnin Tripoli na Libya
Talla

Tuni Amurka ta kwashe Jami’anta daga Libya saboda kazancewar rikici a birnin Tripoli.

A jiya Lahadi akalla mutane 38 aka kashe, yawancinsu Sojoji a musayar wuta da suka yi da Mayaka a birnin Benghazi.

Tun kawar da gwamnatin Kanal Ghaddafi dai a shekarar 2011, gwamnatin Libya ta kasa tabbatar da tsaro a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.